Site icon Muryar 'Yanci

‘Yan Bindiga Sun Harbe Limami Yana Jan Sallar Asham

An harbe wani babban malamin addinin Musulunci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

An yi wa Sheikh Ali Amini, ruwan albarussai yayin da yake jagorantar sallar Asham a ranar Asabar a cikin babban masallacin garin Beni.

Har yanzu dai ba a bayyana wa?anda suka aikata kisan ba.

Tun da farko wasu da ake zargin ‘yan tawayen ADF ne sun kai hari kan wasu ?auyuka biyu a yankin.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce an kashe mutane 19 ciki har da sojoji da dama.

Yayin da ?an ?asar ke ?ara fusata kan yawaitar hare-haren ?an tawaye, shugaban kasar Felix Tshisekedi a ranar Juma’a ya ayyana wani mataki na yi wa lardunan Arewacin Kivu da Ituri ?awanya- matakin da ake ganin zai bai wa sojojin Congo karin karfi da ?warin gwiwa.

Exit mobile version