Wasu da ake kyautata zaton yan fashin jeji ne sun kai hari kan jamian hukumar tsaron farar hula, NSCDC, inda su ka kashe bakwai daga cikinsu a wani wurin hakar maadinai, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa yan bindigar sun rasa mamba guda daya a yayin wani artabu da bindiga a wurin hakar maadinai da wasu yan kasashen waje ke gudanar wa a karamar hukumar.
A cewar majiyar, tuni aka ajiye gawarwakin jamian a asibitin kwararru na Barau Dikko da ke cikin babban birnin Kaduna.

