Shugaban kungiyar wadanda suka damu da alamuran da suka shafi arewacin Najeria, wato (Arewa Citizen Concern for Development) Alhaji RufaI Mukhtar Danmaje ya ce yajin aikin Malam jamioI na shafar alummar arewa ne kawai.
Danmaje na wadannan kalamai ne yayin taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata a nan Kano.
Ya ce laakari da yadda arewacin kasar nan suka dogar da jamioin gwamnati, hakan ta sanya yankin ke shan azaba da yajin aikin.
A cewarsa kudancin kasar nan na da jamioI masu zaman kansu da dama, koda ana yajin aikin ba zai tabasu sosai kamar yadda ya ke taba arewa ba.
Dan maje ya kuma ce yajin aikin na malaman jamioi na daya daga cikin abinda ke dada taazzara matsalar tsaro a arewacin kasar nan.
A cewarsa matasa da dama da basu zuwa makaranta, kuma basu da aikin da za su yi hakan na jefa rayuwarsu cikin matsin da suke shiga harkar taaddanci.
JamiIo basu kyauta mana ba, kuma bamu zaci haka daga wurin manyan jamioin mu ba, kuma arewacin Najeriya ake cuta.
Mune bamu da jamioI masu zaman kansu, mune ke da nakasu kuma mune ake dada haifar mana da wannan balain
Yaran mu da suke zaune a gida dole su kirkiri abinda za su yi, wani in ya samu fitina yenta zai yi
Yana daya daga cikin abinda ya hana mu zaman lafiya, wadannan jamioI da suka ce a tafi yajin aiki, ai arewacin najeriya ake cuta
RufaI Danmaje ya ce a kudancin kasar nan ana samun jiha daya da ke da jamioI masu zaman kansu har guda bakwai, amma da wuya ka samu hakan a arewacin kasar nan.
Ya ce hanyoyin da aka bi aka nakasa arewa na da dunbin yawa, laakari da yadda aka hana wutar lantarki, Ilimi da sauransu.

