Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewa jama’a a jihar sun shiga cikin tasku da kunci biyo bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da kungiyar ?wadago ta kaddamar a fadin Jihar.
Yajin aikin kungiyar na matsayin wani martani ga gwamnatin Jihar ?arkashin Gwamna El Rufa’i domin tursasa shi mayar da ma’aikata sama da dubu biyar da ya sallama daga aiki a kwanakin baya.
Harkoki a jihar sun tsaya cik biyo bayan datse hasken wutar lantarki da hukumar samar da wutar lantarki ta yi tun kwanaki biyu da suka gabata domin marawa yajin aikin baya.
Fitaccen lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana da kungiyar Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond sun soki gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Nasiru El Rufa’i akan abin da suka kira mummunan mataki akan ma’aikata da gwamnan ya ?auka.
Femi Falana da kungiyar ASCAB sun bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufai ya sallami maaikata 60, 000 tun bayan da ya karbi mulkin Kaduna a Mayun 2015.
A wani jawabi da kungiyar ASCAB ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga duk wadanda suke karkashin kungiyar kwadago ta NLC su shiga wannan yajin-aikin. ASCAB ta ce sai an yi da gaske domin ayi maganin sallamar tulin maaikata da talauci da halin rashin tsaron da aka jefa alummar jihar Kaduna a gwamnatin El Rufa’i.
Femi Falana ya ce tun fil azal, maaikatan gwamnati da na masaku ne suka rike tattalin da tattalinarzikin Kaduna. Falana yake cewa a shekarun bayan nan ne duk wadannan ma’aikatu suka mutu, aka kori maaikata daga aiki da-dama ba tare da an biya su wasu hakkokin sallama ba.
Lauyan ya ce a maimakon gwamna Nasir El-Rufai ya yi maganin wannan matsala, sai ya kori maaikata kusan 60, 000, sannan aka hana mafi yawansu hakkin su.
Jihar Kaduna ta na da hadarin zama ko aiki a Najeriya, a dalilin yawan kashe-kashe, garkuwa da mutane, zubar da jini, rikicin kabilanci da addini. Inji Falana SAN.
Har ila yau, Lauyan ya ce ana fama da matsalar tsaro ne saboda yawan korar mutane daga aiki da gwamnati ta ke yi, ya ce keta hakkin maaikata ne ya haddasa hakan.
Lauyan ya ce an kori maaikata 13, 000 a 2016, sannan aka sallami wasu 40, 000 a 2017. Daga nan aka fatattaki malamai 21, 000, a bana kuma an kori maaikata 17, 000. Kawo yanzu akwai maaikata 11, 000 da gwamnati ta shirya za ta kora daga aiki, a cewar Falana.

