Site icon Muryar 'Yanci

Yahaya Bello Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba – Magoya Bayan Tinubu

Wasu daga cikin magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a karkashin tafiyar Tinubu Support Group sun maida wa gwamnan Kogi martani mai zafi dangane da aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin ?asa da sukar Tinubu na ya bar wa Matasa dama.

Kungiyar Tinubu Support Group ta fusata da kalaman da gwamnan ya yi. Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya takalo magoya bayan jigon na APC ne bayan ya yi kira a gare shi ya hakura da n shugaban kasa a 2023.

Tinubu Support Group ta caccaki Yahaya Bello ta ce ya ci amanar tafiyar the Not-too-Young-to-Run domin babu abin da ya tabuka a jihar Kogi na azo a gani wanda har zai cancanci tsayawa takarar shugabancin kasa.

Rahoton yace kungiyar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ta bakin shugabanta, Umar Ibrahim. Da yake jawabi a birnin tarayya Abuja, Alhaji Umar Ibrahim yace duk mutanen Najeriya sun sallama cewa gwamna Bello ya ba matasa kunya.

“Ta ya za mu damka kasa irin Najeriya ga mai ikirarin shi matashin gwamna ne wanda ya damalmala komai da aka ba shi mulkin jiharsa?” “Bello ne gwamnan da ya fi kowane shafe watanni bai biya albashi ba, ya gagara tabuko komai duk da kudin da yake samu a gida da waje.”

“Muna kira gare ka da ka maida hankali wajen kiran mutanen da ka wahalar a jihar Kogi su yafe maka, a maimakon harin kujerar shugaban kasa.”

Kungiyar ta Tinubu Support Group ta ce Bola Tinubu ne wanda ya fi dace wa ya rike Najeriya a 2023, a lokacin da Muhammadu Buhari zai sauka.

Exit mobile version