Site icon Muryar 'Yanci

Yafiyar Buhari Ga Barayin Gwamnati Rashin Adalci Ne – Lauya Falana

Rahotanni daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Shahararren Lauya, Femi Falana, a ranar Juma’a, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bude gidajen yari gaba daya a saki dukkan wadanda aka daure kan laifin sata.

Falana ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron tunawa da marigayi Yinka Odumakin a jihar Legas, Ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi adalci da daidaito tsakanin yan kasa saboda haka wajibi ne a saki dukkan wadanda ke tsare a kurkuku kan laifin sata.

“Najeriya ta zama abin dariya……..Suna yafewa kawunansu, mutumin da yace ya zo yaki da rashawa yanzu shi ke yafewa mutumin da ya wawaure biliyoyin naira.” “Tsokaci na shine kawai a saki dukkan yan ta’adda, barayi dake gidajen yari.”

“Idan gwamnati bata saki sauran ba, zan baiwa lauyoyin sauran dake kurkuku su shigar da kara kotu bisa banbancin da aka nuna.” “Idan za ka yafewa abokanka, wajibi ne dukkan sauran barayin su samu.”

Exit mobile version