Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheik Ahmad Gumi, ya bayyana cewa sun yi tattaunawar fahimtar juna shi da jamian tsaron Najeriya, wa?anda suka gayyace shi dangane da batutuwan matsalolin tsaro.
Bayan amsa gayyatar da Gumi ya yi a ranar Litinin, ya wallafa a shafin sa na Facebook cewa shi fa bai fi ?arfin doka ba, wanda bai aikata laifi ba shi ne bai fi ?arfin doka ba.
Ya ce babu wani abin tayar da hankali dangane da gayyatar jamian tsaro suka yi masa.
Jiya na sha samun kiraye-kirayen wayoyi daban-daban daga abokan arziki da yan jarida, su na tambayar cewa jamian tsaro sun gayyace ni.
To na je kuma sun mutunta ni, a cikin girmamawa, mun tattauna kan batutuwan da suka shafi hanyoyin da za a da?ile hare-haren yan bindiga, kamar yadda kowanen mu ke na sa bakin ?o?arin ta ?angaren sa wajen ganin bayan wannan balai da ya addabi ?asar nan. Amma dai babu wani abin fargaba, ko jayayya ko ?acin rai a ?angaren su. Sun mutunta ni, sun girmama ni.
A ranar Litinin ce kuma Ministan Ya?a Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya bayyana cewa Gumi bai fi ?arfin doka ba, an riga an yi masa tambayoyi.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tuni jamian tsaro suka yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, tambayoyi kan kalamansa na baya-bayan nan kan yan bindiga a Nijeriya.
Ministan Ya?a Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban ?asa a Abuja a ranar Litinin.
A cewar ministan: Gwamnati za ta yi komai don samun duk wani bayani da ake bu?ata don magance matsalolin mu, jamian tsaro suna nan suna aiki.
Sheikh Gumi ko wasu mutane ba su fi ?arfin doka ba. Idan yana da wasu shawarwari ?warara da suka dace kuma masu inganci da jamian tsaro za su yi aiki da su, to za su ?auka, amma idan suna tunanin shi ma yana yin wasu kalamai ne na ganganci, za a tsawata masa. Babu wanda ya fi ?arfin doka.
Idris ya ?ara cewa, Bari in fa?a maku wani abu. Kuma ina sane da cewa jamian tsaro sun gayyace shi don amsa tambayoyi.
Idan ka yi wani kalami musamman kan tsaron ?asar mu, ya zama wajibi jamian tsaron ?asar mu su yi ?arin tunani kan hakan kuma suna yin haka. Babu wanda ya fi ?arfin doka.

