Rahotanni daga birnin Sokoto na bayyana cewar mai alfarma Sarkin musulmi, Muhammad Saad Abubakar ya yi kira akan amfani da ilimin addinin musulunci da na zamani wurin kawo karshen almajirci a arewacin Najeriya.
Mai alfarmar ya yi wannan jawabin ne a ranar kammala wani taro da aka kwashe kwana 2 ana yi akan hanyoyin inganta ilimin Almajirci a jihar Sokoto.
Abubakar ya ce wajibi ne masarautar da sauran su hada kai wurin kawo ci gaba wanda zai kawo karshen barace-barace a jihar Sokoto da arewacin Najeriya gabadaya.
Basaraken ya cigaba da jawabi inda ya ce shi da sauran mutane da dama sun yi ilimin almajirci saidai sun yi shi ne don neman ilimin addini da larabci ba bara ba. Sarkin musulmi ya ce wajibi ne iyaye su dage wurin hana yaran su bara.
Wajibi ne iyaye su tsaya tsayin daka wurin hana yaransu bara. Ko da mu ka je makarantar allo, ba a aike mu bara ba face neman ilimi. Abubakar ya ce wajibi ne a taru a yi hani da aladar bara.
Yayin da yake yaba wa kokarin gwamnatin tarayya wurin taimako ga jamaa, sarkin ya yi kira ga gwamnati wurin sanya kudaden da suka dace wurin inganta ilimi a Najeriya ta hanyar jihohi da kafafen da su ka dace.
Ayi kokarin samar da kudade ga jihohi ta yadda za a inganta ilimi da sauri. Babu abinda ya kai kudi kawo saurin aiki. Don haka idan kowa ya wadata da ilimi, abubuwa da dama za su gyaru.
Anashi ?angaren Gwamna Tambuwal ya ce taron zai samar da nasara Aminu Tambuwal ya bayyana taron a matsayin hanyar samar da nasara. A cewar sa mulkin sa zai taimaka wurin bunkasa ilimi.
Dalilin mu na wannan taron shi ne musamman don kawo hanyoyin da zasu yi gaggawar samar da mafita ne. Ina so in yi godiya ga UNICEF Intervention programme a wurin fannin ilimi a jihar Sokoto.
Gwamnatin jihar za ta samar da kwamiti da za ya zama karkashin shugabancin Malam Lawal Maidoki don kawo canji.
Sakataren kungiyar ilimin larabci da dana musulunci na jihar Sokoto, Dr Umar Aliyu Dandin Mahe, ya ce wannan salon zai dace da salon Indonesia Pondok na gyara ga salon Almajirci.

