Honorabul Lawal Adamu Usman, ya bayyana cewa ya zama wajibi PDP ta kai tikitin takarar shugaban ?asan ta yankin arewa saboda dabarun ya?i irin na siyasa.
Mista LA’ ya yi wannan furuci ne a Zariya, yayin da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ?asa (NAN) ranar Lahadi.
“Saboda dabaru da kuma amfanin jam’iyya da ?asa baki ?aya, ya zama wajibi PDP takai tikitin shugaban ?asa Arewa a babban za?en 2023.”
Mista LA ya bayyana cewa dalilan da yasa ya zama wajibi akan PDP ta fitar da ?an takarar shugaban ?asa daga Arewa shine saboda adalci da dai-daito.
“Saboda adalci da kuma baiwa kowane yanki ha??insa, Arewa ya dace ta fitar da ?an takarar shugaban ?asa a za?en 2023 ?ar?ashin Jam’iyyar PDP.”
“PDP ta shafe shekaru 16 a kan madafun iko, yankin kudu maso gabas sun yi jagoranci na shekara 8 ?ar?ashin Obasanjo, kudu maso gudu sun kwashe shekaru 6 karkashin Jonathan.”
“Amma baki ?aya yankin arewa, arewa ta tsakiya, arewa ta gabas da arewa ta yamma sun yi jagoranci na shekara biyu ne kacal karkashin marigayi Yar’adua.”
Mista LA’ wanda tsohon ?an takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya ne, yace PDP ta fi yawan magoya baya a yankin arewa fiye da sauran sassan ?asar nan.
“Adadin magoya bayan PDP da ake da su a baki ?aya sassan arewa ka?ai sun isa a duba a baiwa yankin tikitin takarar shugaban ?asa.”
“Idan muna son PDP ta farfa?o to wajibi mu lashe zaben 2023, kuma idan muna son cimma haka sai an kai tikiti arewa.”
“Ina da yakinin cewa zamu samu nasara a za?en dake tafe matukar aka tsayar da ?an arewa takarar shugaban ?asa.”

