Site icon Muryar 'Yanci

Wutar Mambila: Dan Kwangila Ne Ya Haifar Da Matsala – Garba Shehu


Gwamnatin Tarayya ?arkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da martani kan wani bincike na musamman da BBC Hausa ta yi kan aikin samar da wutar lantarki a Mambila da ke jihar Taraba.

BBC ta yi tattaki zuwa wurin da aka ware don gina tashar wutar lantarkin Mambila, amma kuma hoton bidiyon da ta dauko daga can ya nuna cewa kwata-kwata ba a fara aikin ba, shekaru 40 bayan fara magana kansa.

A martanin da ya yi lokacin hira da BBC, babban mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan yada labarai Malan Garba Shehu ya ce ”kudin da aka ayyana aikin zai lakume da suka kai sama da dala biliyan hudu bashi ne da zai fito daga bankin China Exim Bank”.

Sai dai a cewarsa takaddama tsakanin gwamnati da wani dan kwangila ya hana bankin ba da bashi.

“Akwai wani dan kasuwa a Najeriya da a ke kira Leno Adesanya, wanda ke ikirarin cewa gwamnatin da ta wuce ta ba shi aikin kawo ‘yan kwangilar da za su yi aikin tashar Mambila.”

Kuma a cewar Malam Garba Shehu binciken da ma’aikatar shari’a a gwamnatinsu ta yi ya nuna cewa “babu inda aka kai kwangilar ofishin tantance kwangiloli don neman amincewa.”

“A kan haka dan kwangilar ya kai gwamnatin Najeriya kara a kwamitin daidaito na ‘yan kasuwa a Paris da cewa yana neman diyyar dala miliyan 200 daga Najeriya kafin ya saki wannan kwangila wanda hakan ya sa China ta dakatar da ba da bashin,” in ji Garba Shehu.

Kakakin ya kara da cewa da zarar kudi ya samu babu bata lokaci ba gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta fara aiki samar da tashar wutar ta Mambila.

“To amma aikin zai yiwu ne idan dan kwangilar da ke ikirarin neman diyya ya nuna kishi ya janye karar da ya kai gwamnati”.

Exit mobile version