Site icon Muryar 'Yanci

Wasanni: Ronaldo Zai Kafa Tarihin Cin Kwallaye

Cristiano Ronaldo ya yi kan-kan-kan a yawan cin kwallaye 109, bayan da ya zura biyu a ragar Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka tashi 2-2 a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Tun farko Ali Daei ne ya ci tawagar kwallon kafar Iran kwallo 109 tsakanin 1993 zuwa 2006, wanda da shi da Ronaldo ne suka ci kwallo sama da 90 kawo yanzu.

Ronaldo mai shekara 36 shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a kungiya a gasar zakarun Turai da ya lashe kofin karo biyar.

A karawar da ya yi da Faransa ya zama kan gaba a cin kwallaye a gasar nahiyar Turai da manyan wasannin tamaula da kofin duniya mai 20 a raga.

Ya kuma kafa tarihin zura kwallaye a gasar nahiyar Turai a wasan da Portugal ta yi da Hungary ranar Talata 15 ga watan Yuni mai 13 a raga.

Shi ne kan gaba a zazzaga kwallaye a gasar kofin duniya da ta nahiyar Turai, wanda ya haura Miroslav Klose mai 19 a raga.

Yawan kwallayen da ya ci wa tawagar Portugal:

31 – Wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

31 – Wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya

19 – Wasannin sada zumunta

13 – Gasar cin kofin nahiyar Turai

7 – Gasar cin kofin duniya

5 – Wasannin Uefa Nations League

2 – Wasannin Confederations Cup

Exit mobile version