Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sallami mai horar da yan wasanta Frank Lampard daga mukaminsa bayan da kungiyar ta tsaya a matsayi na tara a teburin gasar Premier League ta Ingila.
Matakin sallamar Lampard na zuwa ne, bayan da club din ya cimma matsayar a sallame shi saboda shan kaye da kungiyar ta yi har sau biyar cikin wasanni takwas da ta buga.
Lampard ya kasance koci na goma da kungiyar ta Chelsea ta sallama a zamanin Roman Abramovich da ke mallakar kungiyar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Abramovich, ya kwatanta Lampard a matsayin mutum mai sanin ya kamata yayin da yake sanar da korar Lampard, yana mai cewa, a halin da ake ciki, mun yi ammanar cewa abu mafi aala shi ne, mu sauya manajojin wannan club din.
Duk da cewa Chelsea ta lallasa Luton Town a ranar Lahadi don kai wa ga zagaye na biyar a gasar FA Cup, hakan bai sa an ragawa Lampard ba.
Yanzu haka an zabi Thomas Tuchei, don maye gurbin Lampard inda ake sa ran nan ba da jimawa ba za a sanar da nadinsa.
Tuchie ya taba horar da PSG da Borrussia Dortmund.

