Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya sa hannu kan wata sabuwar harkalla da wata kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya bayan kwashe watanni hudu da Kano Pillars.
Kungiyar kwallon kafan ta gabatar da matashin zakaran mai shekaru 28 a duniya bayan an yi masa gwajin lafiya.
Babu shakka wannan makudan kudaden ne suka saka zakaran kwallon kafan ya kasance daya daga cikin ‘yan kwallon kafa da yafi kowa samun kudi a duniya.
Fitaccen dan wasan kwallon kafan ya shiga tsararrakinsa a yayin da yake kokarin farfadowa yayin da a bangaren Super Lig kuwa suke ta shirye-shiryen wasannin 2021-22.
Ya bar kungiyar Al Nassr a shekarar da ta gabata Kafin komawarsa Turai, Musa ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake Saudi Arabia a watan Oktoban da ya gabata kuma yayi yunkurin komawa kungiyar West Bromwich Albion a watan Janairun da ta gabata amma hakan ya gagara.
Kungiyar kwallon kafan ta kasar Turkiyya ta amince da biyan Kwararren ?an kwallon Naira Biliyan guda a duk shekara.

