Bayan tataburzar da ta faru tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da sanannen ?an Kasuwar nan mazaunin garin Kaduna kuma ?an asalin Jihar Katsina Dr Mahadi Shehu, ?an Kasuwar ya tabbatar da cewar yanzu aka fara sabon lale tsakanin shi da gwamnatin Jihar Katsina.
A kwanakin baya ne dai jami’an tsaro bisa ga umarnin Gwamnatin Jihar Katsina suka kama Dr Mahadi Shehu inda aka garzaya dashi Birnin Tarayya Abuja, ya fuskanci gagarumin kalubale da suka ha?a da barazana ga rayuwar shi da sauran abubuwan da suka faru na tashin hankali a gareshi.
Daga bisani Dr Mahadi Shehu ya yi nasara akan Gwamnatin Jihar Katsina a karar da ta shigar a kanshi, inda Kotun daukaka kara ta wanke shi daga dukkanin zarge-zargen da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi mishi.
A zantawar da ya yi da manema labarai a ofishin shi dake Kaduna Dr Mahadi Shehu ya tabbatar da cewar ko ka?an bai razana da barazanar da gwamnatin Jihar Katsina ke yi mishi ba, kuma a halin yanzu ne ya sake ?amarar cigaba da fallasa irin waka ci ka tashi da ake yi da dukiyar jama’ar Jihar Katsina da watsi gami da nuna ko in kula akan rayuka da dukiyoyinsu.
Dr Mahadi Shehu wanda ya koka da shiru da manyan Malamai a Jihar Katsina suka yi akan ta?ar?arewar tsaro a jihar, Malaman da a baya suka yi ma wannan gwamnati kamfe da la’antar gwamnatocin baya na PDP, lallai wannan abin takaici ne da bakin ciki kuma tabbas mutuncin wadannan malamai ya zube warwas a idanun jama’ar Jihar Katsina.
Dr Mahadi Shehu ya sha alwashin cigaba da fallasa zaluncin gwamnatin Jihar Katsina karkashin Gwamna Masari da Sakataren Gwamnatin Jihar Mustafa Inuwa da ‘yan kanzagin su, kuma a shirye yake ya fuskanci dukkanin wata barazanar da za’a yi mishi ko da zata kai ga rasa ranshi ne.
Dangane da batun sace ?aruruwan ?aliban Makarantar kimiyya ta ?an?ara da aka yi da sako su ba tare da ?ata lokaci ba, ?an kasuwar ya bayyana hakan a matsayin wani wasan kwaikwayo da gwamnatin Masari ta shirya, kuma da yardar Allah asirin su zai tonu.
Daga ?arshe Dr Mahadi Shehu ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da Najeriya baki ?aya da su dage da yin addu’o’i akan Allah ya yi musu maganin miyagun Shugabanni wa?anda ke cutar su da zaluntar su, kuma da yardar Allah gaskiya za ta yi halinta, domin zalunci har abada ba zai ta?a dorewa ba.

