Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani rikici mai kama da turnu?u fa?an ibilisai, wai yaro bai gani ba balle ya raba, ya ?arke a Fadar Shugaban ?asa, tsakanin Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Shugaban Maaikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Ibrahim Gambari.
Ministan Harkokin Sufuri Ameachi ya zargi Shugaban Maaikatan Fadar Shugaban ?asa, Gambari da yi masa katsalandan a tsarin bayar da kwangila a maaikatar sa.
Wannan dai shi ne rikici na baya-bayan nan da ya fito fili tsakanin manyan jamian gwamnatin Buhari.
Ameachi dai a cikin wani raddi, ya zargi Gambari da yi masa katsalandan a buga tandar za?en kamfanoni biyu daga cikin kamfanonin da suka nemi a ba su kwangilar Aikin Sa-ido Kan Manyan Jiragen Ruwa Masu Dakon Kaya (ICTN).
Wannan gagarimin aikin kwangila dai a Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa za a yi shi, wadda ke ?ar?ashin kulawar Minista Amaechi.
Binciken mu ya gano cewa Shugaba Buhari da Minista Amaechi sun bayar da kwangilar lamari na tsaro a jiragen da tashoshin ga kamfanoni biyu wato MedTech Scientific Limited da Rozi International Limited.
Binciken dai ya nuna Buhari da Amaechi sun karya doka, ?aida da cancantar bayar da kwangilar ga kamfanonin da ba su cancanta ba.
Kenan an karya ?aidar da ke shimfi?e a cikin dokokin Hukumar Tantance Kwangiloli (BPE).
Yayin da Premium Times ta gano cewa MedTech Scientific Limited kamfanin sayar da magunguna ne, shi kuma Rozi International Limited kamfanin hada-hada da duoalncin manyan gidaje ne.
Amaechi ya samu nasarar kauce wa ?aidar da BPE gindaya, har ya samu Buhari ya sa masa hannun amincewa kan kwangilar.

