An raba rana a tsakanin fitacciyar ‘yar gwagwarmayar nan, Aisha Yesufu da jagoran matasan Inyamurai Nnamdi Kanu, inda suka bu?e wa juna wuta a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Janairu Nnamdi Kanu ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook inda yake nuna jami’an tsaron kudu, ESN, suna hantarar Fulani a sansaninsu dake Isuikwuato, jihar Abia, inda suka yi ta fatattakarsu suna kashe musu shanu.
Wannan bidiyon ya fusata Yesufu, inda ta caccaki lamarin har take cewa hakan bai dace ba. Kamar yadda ta wallafa a Twitter: “Wannan sam bai dace ba. Bai kamata a ce muna daukar doka a hannayenmu, muna kisa da lalata dukiyoyi.
Dole ne mu san yadda za mu dinga hakuri da junamu idan ran mu ya baci. Ya kamata mu dinga bin doka.”
Kanu, a wata takarda da ya wallafa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu ta sakataren shi na yada labarai, Emma Powerful, inda ya mayar da martani yace: “Idan kina daya daga cikin dabbobin da suke ma’adanar dabbobi masu fama da cuta, ina fatan cutar ta kashe ki.
Mu a kudu maso gabas ba dabbobi bane, kuma ba za mu taba zama mu lankwashe kafa ana yi mana yadda aka ga dama ba. Ba za mu taba zama bayi ba, ku tambayi turawa ku ji.
“Ba za mu bar Fulani suna kashe-kashe a yankinmu ba. Za ku iya cigaba da hakuri da azabar da suke yi muku, mu kuwa bamu ga zamu iya ba.
“Kuna ina lokacin da ake yanka mutanenmu, ana yi wa wasu fyade, kuma ana garkuwa da wasu a Isuikwuato?
Masu surutu da hauka irinsu Aisha Yusufu?”
Aisha ta kara da wallafa a Twitter kamar haka: “Ban ga amsar sa ba! Ya je can ya yi wa wahalallun da suke bin shi, wadanda suka gwammaci maye gurbin kwakwalwarsu da burodi, suna neman gindin zama maimakon taimaka wa rayuwarsu, ‘yan wahala.”
Bayan ta ga amsar Kanu, ta mayar da martani, inda tace: “Ku fada wa Shekau din ku na bogi bana daya daga cikin mahaukatan da suke ganin darajar gemunsa da karkataccen jikinsa, wanda hakan yake sanya wa suna bin shi kamar karnuka.”
Ta kara wata wallafa wacce ta caccaki ESN tana nuna rashin dacewar abubuwan da suke yi da kuma wautar masu goyon bayansu.

