Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya aiko sakon taaziyyarsa na rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero, Uwargidan marigayi Ado Bayero sannan mahaifiya ga masu Martaba Sarakunan Kano da Bichi.
A wani bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta na zamani, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da babban rashin da aka yi a Kano.
Da yake jawabi a jiya, Sanusi II ya ce: Mun tashi da rasuwar mahaifiyarmu, Maryam Bade (Ado Bayero), uwargidar marigayi Sarki Ado Bayero.
Tsohon Sarkin ya cigaba da cewa: Ta rasu a kasar Masar, mu na mika taaziyya ga daukacin alumma. da fatan Allah ya sa Aljanna ce makoma Allahumma amin.
Muhammadu Sanusi II ya yi wa marigayiyar addua tare da sauran jamaa. Allah ya sa ta huta, Allah ya sa ciwon da ta yi ya zama kaffara. Sanusi ya ke cewa lallai anyi babban rashin mahaifiyar magajinsa da kuma Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.
Malam Sanusi II wanda ya bar karagar mulki a bara ya sa an yi wa marigayiyar salatin Annabi SAW kafa 10 da karatun suratul Ikhlas domin ta samu ceto.
A karshe bayan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wa Mai babban daki addua, ya kuma yi addua ga sauran wadanda su ka riga mu gidan gaskiya addu’a. Maryam Ado Bayero ta bar Duniya ne bayan kusan shekaru bakwai da rasuwar marigayi Ado Bayero.

