Site icon Muryar 'Yanci

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Ya Rasu

Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Mulkin Sojin Najeriya kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati, Malam Ahmed Joda, ya rasu.

Daya daga cikin ‘ya’yansa, Asma’u Joda, ta shaida wa BBC Hausa cewa mahaifin nasu ya rasu ne a birnin Yola na jihar Adamawa ranar Juma’a.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Alhaji Ahmed Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.

Ya yi aiki a bangarori daban-daban a Lardin Arewa kuma daga bisani ya rike mukamai da dama a gwamnatin tarayya.

Yana daya daga cikin mutanen da ke yi wa lakabi da Super Permanent Secretaries, wato manyan sakatarorin gwamnati, a gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon.

Exit mobile version