Daga Mujaheed Abdullahi Kudan
Garin Kudan yana da kimanin nisan kilomita talatin a arewa maso-gabashin birnin Zariya. Tarihi ya tabbatar da cewa Kudan na cikin tsofaffin garuruwa na Lardin Zazzau, wa?anda suka kafu tun kafin kafuwar birnin Zariya na yanzu, wato tun cibiyar ?asar Zazzau tana Turunku. A yau, Kudan gunduma ce ?ar?ashin hakimcin Maigirma Tukuran Zazzau Alhaji Halliru Mahmud, kuma Kudan ne babban garin da aka ra?a wa ?aramar Hukumar Kudan suna da shi, mai hedikwata a garin Hun?uyi.
Bugu da ?ari, garin Kudan ya yi iyaka da ?aramar Hukumar Danja ta jihar Katsina daga arewa, ta wasu ?auyuka kamar Barmo da Ce?iya da Tudun Kanwa da sauransu. Daga gabas maso arewa ya yi iyaka da garin Sundu ta ?aramar Hukumar Rogo da ke jihar Kano. A gabas kuwa garin ya yi iyaka da ?aramar hukumar Ma?arfi ta Jihar Kaduna. Daga kudu ya yi iyaka da Likoro, daga yamma kuwa garin Kudan ya yi iyaka da garin Hun?uyi wato hedikwatar ?aramar Hukumar Kudan. Haka kuma wasu garuruwa irin su Za?in Kudan da Nassarawan Kudan da ?andako da Ta?an Sani da Sauro da Randa da Damas?e da Fannu da Doka da sauransu, duk sun kewaye garin Kudan ta ?usurwoyi mabambanta.
Wannan yanayi ya sanya duk da garin yana lungu a kan tsohuwar hanyar Zariya zuwa Kano, amma yana da hanyoyi na shiga da fita garin ta kowace ?usurwa, hatta masu harkar simogal idan an rarako su daga hanyar Katsina sukan yi yanke cikin garin domin ?ad-da-sawu.
Kasancewar tun farkon kafuwarsa, wannan gari yana kan iyaka ne tsakanin ?asar Zazzau da Kano da Katsina, hakan ya sanya garin ya sha fama da matsaloli na tsaro tun daga zamanin zaman gargajiya zuwa yau. Garin ya sha fuskantar ?alubale tun daga ya?e-ya?e a lokacin ya?i da hare-hare daga mahara daban-daban, ya zuwa ?ananan tashin tashina na kusa da na nesa.
Game da hare-hare na maya?a, Muhammad (2016) ya tabbatar da cewa Sarkin Mara?i ?anbalkore ya ta?a kawo hari Kudan a kan hanyarsa ta zuwa Zariya domin ya?i, kuma ya babbake garin Kudan ya ?ebi ganima da bayi, inda har ya kama wata mace ya tafi da ita Mara?i har ta haifar masa ?a namiji, amma daga bisani ta dawo Kudan (Muhammad, 2016:7).
Bayan wannan ma, M.G Smith a cikin littafinsa, Government in Zazzau ya ruwaito cewa a tsakanin shekarun 1804-1805 baraden jihadin Shehu Usman ?anfodiyo a hanyarsu ta kai ?auki ?asar Kano wajen Sarki Sulaimanu, sun yi artabu da baraden Kudan kuma suka ?one garin ?urmus, suka wuce Kano (Muhammad, 2016:31).
Ko a zamanin mulkin Sarkin Zazzau Alu ?an Sidi tsakanin shekarun 1903-1920, an ta?a yin wata gobara da ta taso tun daga gabas ta dire yamma, ta ?one garin Kudan ?urmus. A wannan lokaci an yi asarar da ba za ta misaltu ba, domin hatta kaji da agwagi da awaki da sauran dabbobi ba su tsira ba. Maguzawa daga ma?wabta sun sha dabgen mushen da suka ri?a ?iba a sanho(Muhammad, 2016:32).
Abin da yake da muhimmanci game da waiwayen tarihi shi ne sanin irin cikin da jiya ta yi da nazarin yayan da yau ta haifa domin fasalta gobe. Ke nan, barazanar tsaro da hare-hare ba sabon abu ba ne a garin Kudan tun lokacin da duniya take kwance ballantana yanzu da ake bacci da ido ?aya a arewacin Nijeriya. Idan kuwa haka ne, me ke da muhimmanci?
Tarihi ya bayyana a zamanin gargajiya mazauna garin Kudan da mahukuntansu sun yi kyakkyawan tsari na tsaron garinsu daidai da wancan zamanin. Hakan kuma ya rage faruwar balaoi na tsaro a wancan lokacin.
Me ke faruwa yanzu? Gari ya bun?asa, alumma sun yawaita, matsalolin rayuwa da na zamantakewa sun fa?a?a, tsaro kullum yana ?ara ta?ar?arewa, kuma babu wani tanadi ko kulawa ta musamman da mahukunta na zamani suka yi ko suke yi domin da?ile matsalar daidai da zamanin da ake ciki.
A halin da ake ciki yanzu, duk wani mai rufin asiri wanda ya mallaki a?alla Naira Milyan Biyu zaman Kudan ya fi ?arfinsa; ya bar garin. Barin irin wa?annan mutane masu rufin asirin garin kuwa, yana shafar cigaban garin da ?aramar hukumar kai-tsaye da kuma jihar a kaikaice. Domin kuwa ko ba komai hada-hadar kasuwanci na yau da kullum da batun ilimi da tattalin arzi?i kullum dur?ushewa suke yi a garin. Idan aka cigaba da tafiya a haka ba tare da an ?auki mataki ba, tabbas nan da shekara guda garin Kudan zai kasa zauno.
A halin da ake ciki yanzu, an fara bin masu ku?in cefane ne ana kamewa, tun da masu hannu da shunin duk sun bar garin kasancewar babu kyakkyawan tanadi na tsaro.
Kukan mutanen garin Kudan na tsaro ne ba na komai ba. Domin abin ya fi ?arfinsu. Kasancewar garin Kudan yana kan iyakan jihohin Kano da Katsina kuma yana da hanyoyin shiga da fita garin ta kowace ?usurwa kamar yadda aka bayyana a sama, hakan ya sanya a koda yaushe idan ?arayi suka kawo hari garin kafin jamian tsaro su kawo ?auki daga garin Hun?uyi hedikwatar ?aramar hukumar, ?arayin sun gama taadinsu sun fita.
Abin tausayi sama da shekara goma wannan matsala tana faruwa; kullum in ka ji an yi fashi a gabashin birnin Zariya to Kudan ne.
Hakan ya sanya a lokacin wakilcin Isah Muhammad Ashiru a majalisar wakilai ta tarayya aka gina babban ofishin yan sanda a garin Kudan domin samar da wata cibiya ta tsaro da za ta ri?a taimakawa wajen da?ile ayyukan taaddanci a garin da kewaye da ma fa?in ?aramar hukumar. Abin takaici tun bayan saukarsa aikin ya tsaya, an gama ginin har ya lalace ba a kawo maaikata ba kuma kullum matsalar tsaron ?ara taazzara take yi.
A tsawon wannan lokaci, an ta?a kama matar Dagacin Nassarawan Kudan, an kama wani ?an kasuwa mai suna Alhaji Magaji Mai Gya?a, an fitini Sarkin Adon Kudan Alhuslawa da hare-hare har ya bar garin, an kai hari gidan ?anmalikin Kudan har ya bar garin, Madaucin Kudan ma ya bar garin saboda barazanar tsaro. Kwanan nan aka zo har gida aka kashe wani bawan Allah bayan an saci ku?a?e a gidansa. Sannan yanzu haka bayan sati biyar da afkuwar wannan kisa an kai hari gidan wani bawan Allah mai neman na abinci Alhaji Yunusa Garba Wali aka tafi da shi, zuwa yanzu ana zullumin ba a san inda yake ba. Duk wani yun?uri na mutanen gari wajen kai ?auki bai yi tasiri ba domin gaggan mahara ne ?auke da bindigogi na zamani. Kamar koda yaushe, kafin jamian tsaro su kawo ?auki daga Hun?uyi, ?arayin har sun gama taadinsu sun tafi da shi sun fita garin. A wata majiyar ma, an ce jamian tsaron ba su shigo Kudan ba, tsayawa suka yi a Za?in Kudan ba su ?araso ba, sai da ?arayin suka fita.
Domin magance cigaba da afkuwar irin wa?annan matsalolin na tsaro a garin Kudan, kowane ?angare yana da rawar da zai iya takawa, tun daga mazauna garin da mahukunta na gargajiya da yan kasuwa da yan boko da maaikata da yan siyasa da kuma uwa-uba gwamnati.
Abu na farko da ya kamata mutanen gari su yi tare da ha?in kan masu garin shi ne tabbatar da fasalin tsarin zamantakewan garin. Duk sababbin unguwannin da ake da su a na?a masu masu unguwanni domin tabbatar da mazauna unguwannin da kuma samun sau?in gane ba?on da ya shigo da kuma abin da ya shigo da shi, da kuma masu masaukinsa. Za a iya tabbatar da haka wajen sake inganta ala?a tsakanin Sarkin Ba?i da masu unguwanni da Maigari.
Haka kuma a ?auki batun tarbiyya da muhimmanci; ?a na kowa ne, a cigaba da tsawatarwa tare da mulmula tunanin yara masu tasowa domin su zama na ?warai ta yadda ba wanda zai iya yin amfani da su domin fitar da bayanan sirri da zai cutar da garin da ma ?aramar hukumar da ?asa baki-?aya.
Alal ha?i?a, wannan ba zai samu ba sai masu ku?i mazauna da na waje da kuma yan kasuwa sun bayar da gudummawa na ku?i da kayan aiki domin tabbatar da gyara zukatan alumma da kuma tsare dukiyoyi da rayukansu.
Su kuma malaman gari, su cigaba da adduoin da suka saba na neman tsari da kariyar gari. Maaikata da yan boko da yan siyasa da sauran wa?anda ake kira ?anshin gari, su kama hannunmu zuwa inda tsawonmu ba zai kai ba, domin kai kokenmu inda za a share mana hawaye, a samar mana da cibiyar tsaro ba tare da laakari da siyasa ko ?angaranci ba.
Daga ?arshe, idan alumma sun yi nasu, gwamnati ita ce ke da wu?a da nama, ta fi ?arfin kowa kuma muna da ya?inin mafita tana hannunta. A bayyane take, tsawon shekaru bakwai da suka wuce garin Kudan ya kasance koma-baya a duk lissafin ayyukan cigaba a ?aramar hukumar Kudan.
A cire batun siyasa, babu wani abin a-zo-a-gani da za a iya nunawa garin ya amfana da shi. Sai dai akwai abubuwa da yawa wa?anda suka ta?ar?are a garin cikin wannan lokaci, cikinsu kuwa har da batun tsaro. Abin da muka sa rai shi ne, batun tsaro ba a siyasantar da shi. Shi ya sa muka sa rai tsaro zai samu kyakkyawar kulawa a?alla ko ba a tanka ba, musamman a wannan lokaci da matsalar tsaro take cin karenta babu babbaka a arewacin Nijeriya.
A watan da ya gabata, mun ji ?uriyar ?an majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kudan da Ma?arfi ya gabatar da koke a majalisa tare da bu?atar a tabbatar da hukumar yan sanda ta gyara tare da samar da kayan aiki da maaikata a babban caji ofis da aka gina aka banzantar a garin Kudan domin laluben mafita game da matsalar tsaro da take ?ara taazzara a garin. Tun daga wannan lokaci ba mu sake jin wani yun?urin daga wani shugaba ko wanda yake wakiltarmu a kowane mataki ba. Mun koka sosai sakamakon ko jajanta mana ba a yi ba har yanzu, ga shi kuma batun ya cigaba da faruwa.
Da yake mu ne a ?asa, ba za mu yi ?asa a gwiwa ba, muna amfani da wannan dama, muna kai kokenmu ga duk wanda abin ya shafa ko wanda Allah ya ba duk wata dama da zai iya damawa domin damun damuwarmu, tun daga kan Shugaba Muhammadu Buhari da Sufeto Janar na Yan Sandan Nijeriya da Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna da Sanata Sulaiman Abdu Kwari da Hon. Mukhtar Shehu Ladan da Maimartaba Sarkin Zazzau da Alhaji Shuaibu Bawa Jaja da Alhaji Abbas Faisal Likoro da Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Kaduna da Kwamishinan Tsaro na Jihar Kaduna da Maigirma Hakimin Gundumar Kudan Tukuran Zazzau Alhaji Halliru Mahmud da Maigirma Sarkin Kudan Malam Aminu Muhammad Ashiru da duk masu-ruwa-da-tsaki a shaanin tsaro, su taimaka su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro a wannan gari mai matu?ar muhimmanci a dairar ikonsu cikin ikon Allah.
Abubuwan da muke bu?ata daga mahukunta ba masu wahala ba ne, ba su wuce wa?annan ba:
- A cire batun siyasa a shaanin tsaro, a yi laakari da garin Kudan a cushe yake da jamaa masu yawa cikinsa wa?anda kullum suke rayuwa cikin ?ar-?ar na me zai faru cikin dare kafin gari ya waye. Kuma garin Kudan ne aka fi kai hare-hare da sace-sace na dukiya da mutane tsawon shekaru sama da goma a kaf garuruwan gabashin Zazzau. Saboda haka mun ha?ura da duk wani aiki na cigaba, a samar mana da cibiyar tsaro kuma a yawaita jamian tsaro na farin kaya a cikin garin domin da?ile ayyukan taaddanci. Muna da ya?inin hakan ne mafita, domin sai muna da rayuwa da kwanciyar hankali za mu nemi a yi mana titi ko makaranta ko wani abin.
- Idan abu ya faru (muna fatan ya daina faruwar) a?alla ko ba a tanka ba, shugabanni da wakilai su ri?a zuwa suna jajanta mana suna gane wa idanunsu halin da muke ciki. Ta haka ne za su ?ara samun imani da ?warin gwiwar ?aukar matakan kawo ?arshen matsalar.
- A tuna cewa ?aramar hukumar Kudan fa ba ta wasu mutane ?alilan ba ne, aa ta wasu mutane ne ayyanannu cikinsu har da mutanen garin Kudan wa?anda sunan ?aramar hukumar daga sunan garinsu aka samar da shi. Shugabanni da wakilanmu su gane cewa koda ba a ba mu matsayi na musamman ba, to ba mu cancanci a bazantar da mu ba, musamman a kan shaanin tsaro.
- Idan har batutuwa na 1 zuwa na uku ba za su iya samuwa ba. To muna ro?on Sanata Abdu Kwari da Hon. Mukhtar Shehu Ladan su gabatar da wani ?udiri a majalisun ?asa da zai bayar da damar a re?e garin Kudan a ?ara wa ?aramar Hukumar ?anja, tun da mun yi iyaka da Barmo, sai mu koma Katsina. Ko kuma a ?ara wa ?aramar Hukumar Rogo tun da mun yi iyaka da Sundu, sai mu koma Kano kowa ya huta! Idan an yi hakan, muna da ya?inin a Rogo ta Kano ko ?anja ta Katsina, muna da yawan da za a ri?a sauraron bu?atunmu na tsaro fiye da yadda ake burus da mu a ?asarmu ta asali.
- Da yake muna kakar za?e ne, kuma an buga kugen siyasa; duk wanda ke kan mulki kuma yana neman zarcewa to ya sani, in ya zo neman ?uria sai mun tuhume shi a kan irin gudummawar da ya bayar a kan wannan matsala da take ci mana tuwo a ?warya. Idan kuma yanzu mutum yake neman mulkin, sai mun yi yarjejeniya da shi a rubuce a kan abin da zai yi mana a kan wannan matsala da ma wasu da suke damun mu. Idan kuma aka hana mu damar tambayar ?an takara wajen ya?in neman za?e, to tabbas za mu tambaye shi a akwatun za?e. In ya so, ko da mutum zai ci, to ya ci ba tare da ?uriunmu ba. Hakan zai rage mana ra?a?in mun za?i mutum ya yi burus da rayuwarmu a lokacin da muke fuskantar barazanar tsaro.
Daga ?arshe, muna kira ga alumma da kuma gwamnati da a yi duk mai yiwuwa wajen da?ile wannan matsala tun kafin ta da?ile rayuwarmu a mahaifarmu. Domin kuwa ko ba komai icce tun yana ?anye ake tan?wasa shi, to mu namu iccen ya fara bushewa, gab yake da karyewa. Shi kuwa tsaro ba a wasa da shi, domin idan an san farkon matsala ba a san ?arshenta ba.
Muna fata kamar yadda harin Sarkin Mara?i ?anbalkore ba ta ?arar da garin Kudan ba; kamar yadda gobarar Kudan da sauran fitintinu na zamanin da ba su ?arar da Kudan ba, wannan ?alubale ma zai wuce ya zama tarihi.
Allah ya cigaba da kare bayinsa.

