Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Nijeriya ba ta da shugabancin da ake bukata domin tunkarar kalubalen rashin tsaro a kasar.
A yayin da ake zantawa da shi a shirin ‘Sunday Politics’ a gidan talabijin na Channels, a ranar Lahadi, Lamido ya ce ya zama dole gwamnati ta rika fadawa mutane gaskiya kan halin matsalar tsaro da kasar ta tsinci kan ta a ciki.
“Ya kamata mutane su rika bibiyar gwamnati kan alkawurran da ta yi kuma bana son ya zama kaman na saka siyasa cikin lamarin amma gaskiya ne. Idan kana neman mulki na siyasa ya kamata hanyar samun ya zama nagartace.”
“Ya kamata mu ajiye siyasa a gefe. Mene mu ke yi a matsayin mu na shugabanni? Ba mu da shugabanci a Nigeria, wannan shine matsalar kuma duniya na kallon mu. “Fiye da komai, matsalar shine shugabanci.
Shugabanci na gari na da matukar muhimmanci. Me yasa Zamfara ke zama matattaran ta’addanci a Nigeria, Me yasa?” Jam’iyyar APC ta nemi mulki ne ba tare da sanin abin da za ta aiwatar ba”.
Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan Ya ce: “Sun san karya suke yi. Kafin nan, mulki kawai ake so. Sai bayan sun samu mulki sannan suka fara tambaya, me za mu yi? Don haka tun farko ya kamata a saka adalci a lamarin.”
“Batun shine halin yi wa matasa karya. “Idan ka saka musu rai cewa gwamnati za ta taimaka musu, ka samu gwamnati kuma ka gaza biya musu bukatunsu, za a samu matsaloli.”

