Site icon Muryar 'Yanci

Tsagerun Yarbawa Sun Ayyana Korar Fulani Daga Yankin Ranar Litinin

Tantagaryar ?an iskan yankin Yarabawa, mai ?aukar doka a hannun sa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bai wa dukkan Fulani makiyaya mazauna jihohin Yarabawa wa’adin daga ranar Litinin mai zuwa ba ya son ganin ko Bafulatani makiyayi ?aya tal a jihohin yankin.

Wannan sabon garga?i ya fito ne a wata tattauna da Kakakin Ya?a Labaran sa, Oluyomi Koki ya yi da shi kuma ya watsa ga manema labarai a ranar Laraba.

“Mu na sanar da cewa daga ranar Lininin mai zuwa, ba mu son ganin ko da Bafulatani makiyayi ?aya tal a cikin jihohin Ekiti, Lagos, Oyo, Ogun, Ondo da Osun.

“Kuma daga nan ni ma zan ri?a fita mu na fatattakar duk wanda ya ?i ficewa.

“Daga ranar Litinin kada mu ?ara jin labarin an yi garkuwa da wani Bayarabe ko ?aya.

“Zan kara?e dukkan dazukan jihohin Yarabawa domin na tabbatar babu wani makiyayi Bafulatani da ya ragu cikin dazukan wa?annan jihohi.”

Igboho dai ya ce bai yiwuwa a ce wasu tsirarun ?abila ba su wuce su miliyan shida ba, amma su addabi mutum kusan miliyan 250.

Har yau dai jami’an ‘yan sanda ba su kama Sunday Igboho ba.

Exit mobile version