Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sakataren APC na ?asa, Surajudeen Basiru, ya bayyana cewa jadawalin ?ididdigar malejin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci a Najeriya, wanda Hukumar NBS ta fitar kwanan nan, akwai ?arin gishiri da zuzuta al?aluma a cikin bayanan.
Basiru ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba, lokacin da ake tattauna da shi a Gidan Talabijin na Channels.
Basiru wanda lauya ne kuma tsohon Sanata, ya yi wannan bayanin daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ta ?o?arin kwantar wa matara hankali don kada su fita zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa.
Cikin makon jiya ne dai NBS ta fitar da sabuwar ?ididdigar malejin tsadar abinci, wanda ta ce ya dangwale kashi 40.87, yayin da burkin ha?urin yan Najeriya ya tsinke daidai gangara.
Jadawalin tsadar rayuwa da ra?a?in hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi wanda Hukumar ?ididdigar Al?aluman Bayanai ta ?asa (NBS) ta fitar ranar Litinin ?in nan, sun nuna cewa malejin tsadar kayan abinci ya dangwale zuwa kashi 40.87% bisa 100% a watan Yuni, 2024.
Hakan na nuni da cewa ya ?aru da kashi 15.62% bisa 100% idan aka kwatanta da gejin sa na watan Yuni 2023, inda a lokacin yake daidai kashi 25.25% bisa 100%.
Haka kuma NBS ta ce malejin game-garin tsadar rayuwa ya haura zuwa kashi 34.19% bisa 100%.
?ididdigar ta NBS, wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, tattabar da cewa tsawon watanni biyar kenan aka shafe duk wata kayan abinci da kayan masarufi na fuskantar tashin farashi.
Najeriya ce dai ?asa mafi ?arfin tattalin arziki a Afrika, kuma ?asa mafiya yawan jamaa a Afrika.
Sai dai kuma yan ?asar sun afka cikin masifar tsadar rayuwa tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, a ranar 29 ga Mayu, 2023 tun a wurin da aka rantsar da shi.
Tsadar rayuwa ta ?ara tsamari yayin da gwamnatin Najeriya ta yi sagegeduwar sakacin da darajar Naira ta karye a kasuwar canjin ku?a?en waje.
Duk da masifar tsadar rayuwa da ake fama a ?asar, har yau ana kiki-kaka wajen kasa samun matsaya dangane da batun ?arin mafi ?an?antar albashi, wanda fiye da shekara ?aya ake ta tsallen-gada a kan sa.
Wannan sabuwar ?ididdiga ta NBS, ta zo yayin da yan Najeriya ke ta kartar ?asar furucin shirin fitowa su yi wa gwamnati zanga-zanga a ?arshen watan Yuli.
Idan aka kwatanta malejin tsadar rayuwa na watan Yuni 2023, za a ga ya tsaya ne daidai kashi 22.79. Yanzu kuwa a Yuni 2024, ya dangwale zuwa kashi 33.95, inda cikin shekara ?aya aka samu ?arin gwauron tashi da kashi 11.40.
Sai dai sakataren na APC ya ce a yanzu ya tabbatar idan za a sake wata ?ididdigar, to za a ga cewa an samu rangwame.
Ya ce shi da kan sa ya ga ?ididdigar NBS, kuma ya ga cewa tsadar rayuwa da tsadar abinci ya yi sau?i sosai daga watanni hu?u zuwa yau.

