Wata sabuwar ?ididdigar da Ofishin ?ididdigar Al?aluman Bayanai ta ?asa ta fitar, ya nuna cewa tsadar farashin kayan abinci da kayan masarufi ya cilla har zuwa ?aruwa da kashi 37.92 a cikin watan Fabrairu.
Amma malejin tsadar rayuwa a cikin watan Fabrairu ya ?aru zuwa kashi 31.70, idan aka kwatanta da kashi 29.90 na tsadar rayuwa daga Janairu, kamar yadda NBS ta fitar a ranar Jumaa.
Wannan ?ididdigar ta nuna cewa cikin watan Fabrairu 2024 tsadar rayuwa ta ?aru da kashi 1.80, idan aka kwatanta da Janairu, 2024.
NBS ta ce hauhawar farashi da tsadar rayuwa sun tashi sosai a 2024, idan aka auna da watan Fabrairu 2023 inda ya ke a kashi 9.79, wanda a wancan lokacin maleji ya na kashi 21.91.
Tuni dai ababen more rayuwa suka gagari talaka, inda su kan su masu hali da masu ?arfin halin sayen wasu kayan amfanin gida su ka fara ha?ura.

