Shugaban kamfanin Lamama Biredi a Jihar Katsina, Alhaji Adamu Abdullahi wanda yayi shekaru masu yawa yana
sana’ar samar biredi a kamfaninsa na Lamama dake garin Magama-Jibiya a karamar hukumar Jibia ta jihar katsina, ya bayyana hauhawar farashin flour da sauran kayayyakin masarufi a Najeriya cewa gwamnati ce sanadi.
A cewarsa “Matukar Gwamnati za ta maida hankali zuwa fage na kasuwanci tare da bada gudunmuwa ta musamman ga ‘yan kasuwa tare da rage yawan harajin da suke biya, kuma ta samar da wadatattun daloli ga masu fita kasashen ketare domin siyo kayan aiki; babu shakka hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da harkokin kasuwanci ke fuskanta.”
“Taimakawa masana’antu zai taimaka wa Gwamnati wajen farfado da tattalin arziki tare da magance zaman banza. Amma idan har aka ce za ayi watsi da sha’aninsu, kamfanonin za su durkushe a karshe kuma zaman banza ya kara yawaita cikin kasar.” Inji shi.
Alhaji Adamu Lamama, ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da wakilinmu Abdulrazak Ahmad Jibia, ranar laraba, 7 ga watan Oktoba, 2021, inda ya kara da cewa tuni kungiyar masana’antun biredi ta najeriya ta shirya tsaf domin shiga yajin aiki, amma dai har yanzu ba’a bayyana rana ba a sakamakon wata ganawa ta sirri dake gudana a halin yanzu tsakanin wakilan masana’antun biredi da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a Majalissar wakilan Najeriya.

