Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya daga tafiyar da ya yi zuwa ?asar Waje a ranar Talata, 27 ga watan Yunin 2023, idan har ba wani sabon sauyi aka samu ba.
Shugaban zai shigo Najeriya ne ranar Talata ana gobe bikin shagalin babbar Sallah wacce za a gudanar ranar Laraba 28/6/23.
Wani majiya ta kusa da fadar shugaban ?asa ta tabbatarwa da Channels tv a ranar Lahadi cewa, shugaban ?asar a birnin Legas zai yi hutun Sallah.
A cewar majiyar, tuni har an tura da tawaga zuwa birnin na Legas domin tarbar shugaban ?asar idan ya duro Najeriya.
A ranar Juma’a, Tinubu ya kammala ziyarar da ta kai shi birnin Faris na ?asar Faransa, inda ya halarci taron ?oli na ku?i na duniya da aka gudanar a ?ar?ashin jagorancin Emmanuel Macron.
Tun da farko, an shirya cewa shugaban zai dawo Najeriya ne a ranar Asabar, amma sai jirginsa ya shilla zuwa birrnin Landan na ?asar Ingila domin wata ?ar gajeruwar ziyara ta ?ashin kansa, kamar yadda hadimin shugaban ?asa Dele Alake, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

