Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Laraba a jihar Kano, ya bayyana fatansa na ganin jamiyyarsa za ta lashe jihar Kano da Najeriya baki daya, a zaben 2023.
Tinubu, wanda alummar jihar suka yi masa gagarumin tarba, ya je Kano ne domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na Arewa maso Yamma.
Ya godewa alummar jihar bisa gagarumin fitowar da suka nuna, goyon baya da hadin kai.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kira ga magoya bayan jamiyyar da su zabi APC tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa.
Ya kuma tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC cewa kuriun mutanen Kano na APC ne, inda ya ce jamaa sun ga ribar dimokuradiyya da gwamnatin APC ta samar.
Gwamnan ya ce jamiyyar ta amince kuma ta samu kwarin guiwar dimbin jamaa da suka tarbi Asiwaju Bola Tinubu a Kano.
Nasarar da aka samu taron bayyananne ne da kuma nuna fifikon mutanen Kano dangane da zabin da ke gabansu.
“Goyon bayan Gawun/Garo kuri’ar amincewa ce ga dan takarar gwamna da mataimakinsa,” NAN ta ruwaito na cewa.
Ganduje ya ce Tinubu yana da hali, iya aiki da kuma cancantar samar da shugabanci da kowa zai yi alfahari da shi a kasar nan.

