Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Dan takarar shugaban kasa na jamÂiyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya daga kasar Faransa.
Tinubu ya bayyana haka a shafin sa na Tuwita, da Instagram a lokacin da jirgin nasa ya sauka Najeriya da yammacin ranar Asabar.
Tinubu ya bar Najeriya ne jim kadan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar 27 ga watan Yuni.

