A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Tinubu ya ce An baiwa hedikwatar tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaro cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan aika-aika da aka yi wa alummar Najeriya. Ya kuma bayyana kisan a matsayin jahilci.
Ya kuma mika taaziyyarsa ga iyalan sojojin da aka kashe tare da bayyana aniyar gwamnatinsa na hukunta wadanda ke da hannu a kisan sojojin.
Shugaban ya ce, Wannan lamarin, ya sake nuna irin hatsarin da maaikatanmu da mata ke fuskanta a bakin aiki. Ina jinjina wa jarumtarsu da jajircewarsu game da kishin kasa.
A matsayinmu na alumma, dole ne mu ci gaba da tunawa da kuma karrama duk wadanda ke bai wa kasarmu kariya. Dakarunmu da suka mutu a yankin Okuama sun bi sahun yan mazan jiya.
Jamian sojojinmu su ne jigon kasarmu. Duk wani hari da aka kai musu hari ne kai tsaye ga alummarmu. Ba za mu yarda da wannan danyen aiki ba.
Na bai wa hedikwatar tsaro da babban hafsan soji cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan laifi.
Gwamnatina ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane yanki na Najeriya.
Dakarun sojin da aka yi wa kisan gilla a kauyen Okuama dake karamar hukumar Ughelli ta kudu a yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya, sun hada da Babban Kwamanda guda, Manjo biyu da Kyaftin guda da kananan sojoji 12 har da farar hula daya.

