Site icon Muryar 'Yanci

Tattalin Arzikin Najeriya Na Dab Da Rushewa – Masana

Yayin da Najeriya ke shirin za?en 2023 cikin shekara mai zuwa, hujjoji na ?ara bayyana cewa tattalin arzikin ?asar fuskantar matsanancin yanayi biyu: wato baitilmalin da ba ko ranyo a ciki, sai kuma raguwar da tattalin ke yi a kullum.

Jami’an gwamnati da manyan ‘yan kasuwar da ke da masaniyar halin da ake ciki, sun ce ana nuna damuwa sosai a Abuja da Legas, yayin da wani za?a??en jami’in gwamnati ya jawo hankalin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele cewa abin da ya rage a asusun Najeriya da ke waje fa bai wuce dala biliyan 15 ba, wato ?asa sosai da dala biliyan 36 ?in CBN ?in ya yi i?irarin cewa su na cikin asusun.

Yayin da Najeriya ta kashe naira tiriliyan 5.9 wajen shigo da kayayyaki daga waje tsakanin Janairu zuwa Afrilu 2022 ka?ai, dala biliyan 15 kacal ?in ?asar ke da shi a yanzu ba su wuce kashewa cikin watanni hu?u ba kenan wajen shigo da kayayyaki.

Masana harkokin tasarifin ku?a?en sun ce da a ce komai na tafiya daidai, to raguwar ku?a?en ba abin damuwa ba ne. Amma abin fargabar shi ne yadda aka shafe watanni shida cur Najeriya ba ta zuba ko sisi a cikin asusun don ku?in su ?aru ba. Wannan kuma ya faru ne saboda matsalar rashin wadatar ?anyen man da Najeriya ke fitarwa waje ne, da kuma tsayuwar gwanin jakin da kasuwar ta yi.

Sannan kuma ?aukar lokaci mai tsawo da NNPC ta yi ta kada zuba cinikin ?anyen mai a CBN, shi ne ya haifar da tsawwala farashin dala a kasuwannin ‘yan canji.

Wata babbar ma’aikaciyar banki wadda ta ce wannan jarida ta rufa mata asiri kada ta ambaci sunan ta, ta ce an da?e ana ?oye gaskiyar sauran adadin ku?a?en gwamnati a cikin asusun waje, wanda babbar matsala ce sosai a halin yanzu.

Ta ce an yi ?arin gishiri ne wajen ainihin yawan ku?a?en da ke CBN, domin kawai a ?oye ainihin adadin da su ka rage a asusun waje.

An ha??a?e cewa wannan babban jami’in gwamnati wanda kuma za?en sa aka yi, ya sanar wa Shugaba Muhammadu Buhari gaskiyar halin da ake ciki na ramewar tattalin arzikin Najeriya. Sai dai kuma Fadar Shugaban ?asa ba ta amsa wa PREMIUM TIMES tambayoyin da ta yi kan wannan mawuyacin halin da ake ciki ba.

Sannan kuma maida NNPC hannun jarin masu kasuwanci da aka ce an yi, ya ?ara dagula matsalolin. Wato tunda NNPC ya kasa zuba ku?a?en cinikin ?anyen mai ko na fetur a asusun CBN, tilas kenan bankin ya tashi ya nemi inda zai samu manyan ku?a?en ?asashen waje.

Exit mobile version