Site icon Muryar 'Yanci

Tashin Hankali: Matashi Ya Babbaka Uwarshi Har Lahira A Jihar Neja

Mazauna unguwar Darusalam da ke Minna, Jihar Naija sun tashi cikin ka?uwa da firgici bayan da wani matashi, mai suna Steven Jiya, ya bankawa mahaifiyarsa, Comfort Jiya wuta.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a ranar Litinin ?in da ta gabata ne dai Steven, wanda ?an ?waya ne, ya dawo da ga garin Suleja a Jihar Naija ?in dai, inda bayan ya dawo gida ne, sai kawai ta raya masa cewa ya ?ona mahaifiyarsa.

Jaridar ta ce a lokacin Comfort, wacce tsohuwar Shugabar makarantar sakandire ce, tana tsaka da girki a kicin, sai kawai wannan tamba?a??en ?a ya zazzaga mata fetur ya kuma cinna mata wuta a gidanta da ke unguwar Darusalam ya kuma tsere.

Nan fa ta fito a waje tana ihu a kawo mata ?auki, inda kan ka ce kwabo, wutar ta ?one mata ilahirin jikinta.

Wata majiya a dangin marigayiyar ta ce an garzaya da ita asibiti inda ta ke jiyya.

Sai dai kuma, da misalin ?arfe 3 na yammacin jiya Juma’a, marigayiya Comfort ta ce ga garin ku nan.

Wata majiyar ta ?ara da cewa dama can Steven fitinanne ne kuma ya yi yun?urin hallaka uwar tun a baya.

Jaridar ta ce ta tuntu?i rundunar ?an sanda ta Naija amma ha?ar ta ba ta cimma ruwa ba.

Sai dai kuma, in ji jaridar, tuni dai ?an sandan Caji-ofis na Minna su ka samu nasarar dam?e Steven kuma har an kai shi babbar kotun Minna inda zai girbe abin da ya shuka.

Exit mobile version