Site icon Muryar 'Yanci

Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Sace ?an Majalisa

Rahotanni daga Jalingo babban birnin Jihar Taraba na bayyana cewar wasu : Yan bindiga wa?anda ba’a san ko su wanene ba ?auke da muggan makamai sun sace ?an Majalisar dokokin jihar mai suna Barista Bashir Muhammad a kofar gidan shi dake Jalingo a daren jiya.

Da misalin kusan karfe 1:45, Yan bindigar suka yi garkuwa da Dan majalisar Barista Bashir Mohammed, mai wakiltar Nguroje a Majalisar Dokokin Jihar Taraba.

Da yake bayyanawa manema labaru shugaban kwamitin ya?a labarai na majalisar, kuma Dan’uwa ga Dan majalisar wanda rahoton ya buye sunan sa, ya ce an ?auke shi ne a gidansa da ke kusa da Filin Idi na Dr Jalo a garin Jalingo.

Kafar turanci ta Channels ta ce Mutumin ya bayyana cewa babu alamun jami’an tsaro a lokacin da ‘yan bindigar suka je tafiya da shi, wanda aka yi kusan awa uku ana artabu.

Exit mobile version