BASHIR ADAMU, JALINGO
Labarin dake shigo mana daga Jihar Taraba na bayyana cewar Gidauniyar FHAMAS Cancer Foundation dake da Shalkwata a Jalingo, ta gina Fanfon Bur-tsatse (Borehole) kyauta a Kauyen Bakin-Dutse, dake Karamar Hukumar Ardo-Kola.
Al’ummar Kauyen Bakin- Dutse, dake Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba sun nuna farin cikinsu, bisa tallafin da suka samu na Famfon Bur-tsatse da Gidauniyar FHAMAS Cancer Foundation tayi musu kyauta
Da yake kaddamar da fanfon ga Al’ummar yankin Bakin-Dutse, Shugaban Gidauniyar, FHAMAS Cancer Foundation, Dr. Alex Maiangwa yace sun yanke shawarar yin aikin ne duba da ganin irin yadda Al’ummar ke fama da Wahalan rashin ruwa a yankin. Kuma “zamu cigaba dayin wasu ayyukan jin-kai kamar yanda muka fara, muna fatan Al’ummar da sukaci gajiyar irin wadannan ayyukan zasu cigaba da bamu hadin kai da goyon baya”.
Shugaban Karamar Hukumar Ardo-Kola, Isma’il Zakari (Dangote), shine ne ya karbi Fanfon Bur-tsatsen a madadin Al’ummar ta Bakin-Dutse, ya nuna farin cikinsu matuka tare da shan alwashin cewa zasuyi dukkanin mai yiyuwa a Matakin Karamar Hukuma wurin tabbatar da kulawa dashi.
A bayanansu maban-banta, Al’ummar Bakin Dutsen dasukaci gajiyar aikin sun nuna farin cikinsu matuka, musamman ga mai Gidauniyar FHAMAS, Hajiya Hadiza Bello Yero kan zakulo yankisu da tayi domin kafa Katafaren Cibiyar Gwaji da jinyar Cutar Daji (Cancer) na Kasa da Kasa, hade da wurin cin Abinci na zamani “mun tabbatar miki da cewa, bazamu baki kunyaba, a shirye muke, kin samu hadin kan mu dari bisa dari, wurin taimakawa dukkanin ayyukan da kikasa a wurin mu, kuma ko shakka babu da yardan Allah zakiyi nasara”, kuma “zamu kula da Fanfon Bur-tsatsen da kika gina mana, bazamu barshi a wulakance ba, wannan shine karo na farko da muka sami irin wannan abin arzikin”.
A nata bangaren, Memba a Gidauniyar FHAMAS,Uwargida Sera David Ibbi, tayi karin haske dangane da ayyukansu na jin kai ga Al’ummah, tana mai cewa ” Ciwon Daji, ciwo ne da ya addabi Al’umma a Kasannan, kuma “Mai FHAMAS, Hajiya Hadiza Bello Yero, ta taba kamuwa dashi, tayi jinya har ta warke, na daga cikin dalilan da yasa ta kafa wannan Gidauniya kenan, wanda in Allah Ya yarda duk wani mai fama da ciwon Daji, wato Cancer a Turance, zaici gajiyar jinya a wannan Gidauniya, ta kuma “ce Zuciyar Jajiya Hadiza na Alkhairi ga Al’ummah, musamman mabukata, kuma tacigaba da wadannan ayyukan na jin-kai, Allah zai biyata”.
Da take nata bayanin, wacce ta kafa Gidauniyar FHAMAS Cancer Foundation, Hajiya Hadiza Bello Yero ta roki Al’ummar Kauyen Bakin-Dutse da su tabbata sun kula da wannan Fanfon Bur-tsatse da kyau, “Mata sune sukafi wahala wurin neman ruwan dazasuyi aikin gida, saboda haka ku Mazaje, ku kula, kar ku bar Kanan Yara su rinka wasa dashi, domin a karshe, idan ya lalace, Iyaye Mata ne zasu wahala; Hadiza Bello Yero ta kuma rokesu da su kula da dukkanin kayayyakin aikin da suka kawo wurin, su tabbata basu bar kowa ya sata kayan ba, domin ta haka ne kawai zata sami kwarin guiwar cigaba da sauran ayyukan da tafara”,
“Idan Allah Yasa mun kammala wannan Cibiyar Jinyar Cutar Daji (Cancer), burinta shine, bama Jama’an Kasar kadai zasuci gajiyar jinyar ba, harma daga Kasashen Turai zasu garzayo jinya, saboda ingancin Cibiyar, da Yardan Allah.

