Wasu da ba a san ko su waye ba, sun sace shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Taraba mai suna kwamred Peter Jediel.
An sace shugaban kungiyar ne da sanyin safiyar lahadin a gidansa da ke yankin Sunkani karamar hukumar Ardo-Kola.
Kanin shugaban kungiyar Mr Fidelis Jediel ya shaida wa yanjarida cewa yan bindigar sun mamaye hanyar zuwa gidan, suka yi awon-gaba da shi.
Har ya zuwa lokacin hada labarin, babu wata tartibiyar magana daga hukumar yansandan jihar.
Harkar satar mutane tare da yin garkuwa da su na nema zama ruwan dare a yankin Arewacin Najeriya, inda a kusan kullum ‘yan Bindiga wa?anda ake kyautata zaton cewa Fulani ne ke afka wa jama’a suna kisa da satar su.
A kwanakin baya ‘yan Bindigar sun sace wani Shugaban ?aramar Hukumar a Jihar Taraba, kuma suka kashe shi daga baya, lamirin da ya sanya Gwamnan jihar Darius Ishaku ya fito ya yi kiran da a bar ‘yan Najeriya su mallaki Bindigogi domin kare kansu.

