Site icon Muryar 'Yanci

Tambuwal Ya Rasa Matsayinsa Na Shugaban Gwamnonin PDP

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jim kadan bayan da gwamnan jihar Sokoto Tambuwal ya sauka daga mukamin shugaban gwamnonin PDP, an sanar da gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Gwamnan Oyo ya zama sabon shugaban gwamnonin PDP ne a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba a taron majalisar zartaswar PDP da ya gudana a Abuja.

An bayyana Makinde a matsayin sabon shugaban kungiyar ne mintuna kadan bayan da Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yin murabus.

Exit mobile version