Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi al?awarin cewa dukkan jihohi 36 da ?asar nan da kuma yankin Abuja za su amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na Agajin Kyautar Ku?i ga Matan Karkara, wato ‘Special Cash Grant for Rural Women’.
Ta bada wannan tabbacin ne a wajen taron ?addamar da shirin a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ranar Alhamis, 3 ga Disamba, 2020.
A jawabin da ta gabatar a taron, ministar ta ce al’ummar Jihar Imo su ma masu cin moriyar shirin nan ne na tura wa mata agajin tsabar ku?i, wato ‘Conditional Cash Transfer’ wanda aka ?auki gidajen marasa galihu guda 11,697, da shirin N-Power, da shirin ciyar da ?alibai da ke zaune a gida (Home Grown School Feeding) da kuma shirin tallafin yin sana’a na GEEP, wato ‘Government Entrepreneurship Empowerment Programme’.
Sadiya ta ce, Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi maida hankali ga matsalolin marasa galihu a ?asar nan tun daga 2015 kima mutum 150,000 ake sa ran za su ci moriyar shirin ta na bai wa matan karkara tallafin ku?i a dukkan ?ananan hukumomi 774 da ke ?asar nan.
Tun daga farkon shirin nan na ‘National Social Investment Programme’ a matsayin wani tsari na ya?ar talauci a tsakanin yawanci al’ummar mu, rayuwar talakawa fa?irai a Nijeriya ta inganta sosai. Da yawa daga cikin irin wa?annan mutanen sun samu cikakken sauyin rayuwar su. Saboda haka, ina farin cikin ganin taruwar ku a nan domin ?addamar da shirin Gwamnatin Tarayya na raba wa matan karkara agajin ku?i, wanda ya na daga cikin shirye-shirye masu yawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu ta fito da su saboda ta ?aga rayuwar yawancin jama’a daga ?uncin rayuwa.
Ministar ta ?ara da cewa manufar wannan agajin musamman ?in ita ce a kai tsabar ku?i kai-tsaye ga gidajen da su ke bu?ata wanda hakan zai taimaka wa iyalan wajen sayen kayan masarufi, yin amfani da kayan magance matsalar yunwa sayen kayan abinci da kula da lagiyar jiki, da shigar da yara da biya masu ku?in makaranta da dai sauran su.
Ta yi kira a gare su da su yi amfani da ku?in wajen yin ?ananan kasuwanci wanda hakan zai taimaka wa dogaro da kai da samun sana’a.
Tun da farko, sai da mai ba Gwamnan Imo Shawara kan shirye-shiryen cigaban al’umma na SDGs da ayyukan jin?ai, Gimbiya Christina Udeh, ta ce ziyarar da ministar ta kai a jihar, shaida ce da ke nuna yadda ta ke damuwa da matsalolin tattalin arzikin al’ummar Jihar Imo, ciki har da na?asassu da fa?irai da ke zaune a yankunan karkara.
Ta ce, “Shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na bada tallafin ku?i ga matan karkara zai rage fatara da yunwa, ya hana marasa galihu cigaba da fa?uwa cikin ramin fatara da yunwa kuma ya ba su kariya daga bala’o’i.
“Haka kuma ministar ta zo nan ne domin ta ?addamar da Ranar Mutane Masu Fama da Nakasa ta Duniya sannan ta raba N20,000 ga kowace macen karkara domin ta ja jari wanda zai taimaka ya sauya mata rayuwar ta da halayya.
Daga bisani ministar ta mi?a tsabar ku?i ga wasu daga cikin matan karkarar.
Matan sun bayyana godiyar su ga Shugaba Buhari saboda wannan tsari da ya fito da shi.

