Site icon Muryar 'Yanci

Ta’addanci: Ana Wuce Gona Da Iri Wajen Kama Fulani – Gumi

Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare hakkin Makiyaya a Kaduna, Dr Ahmad Gumi ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare hannun jami’an tsaro.

Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar.

“Kwanaki kadan da suka gabata, wani mutum ya kira ni ya ce jami’an tsaro sun kama yara bakwai da ba su aikata laifi ba a ranar 17 ga watan Mayun 2022 kuma tun ranar babu labarinsu. Akwai kuma labaran batar matasan Fulani da yara ba tare an sake ganinsu ba.

“Akwai wadanda ake tsare wa ko a tura gidan yari na shekaru babu shari’a. Idan wani ya aikata laifi, doka ya ce a kai shi kotu cikin awa 24 amma ana ajiye matasan nan tsawon shekaru babu shari’a, wasu sun mutu a tsare.

Bai kamata wannan na faruwa a kasar nan ba. “An kafa kungiyar Nomadic Right Concern Group ne don nema wa yaran da aka kama ba tare da laifi ba adalci. Wadanda aka samu da laifi a hukunta su yadda doka ya tanada amma wadanda ba su da laifi a sake su saboda adalci da daidaito.

Ya yi bayanin cewa cikin ayyukan kungiyar, akwai gano adadin yaran Fulani wadanda ake tsare da su kuma ba su da laifi da neman lauyoyi da za su fitar da su.

Da ya ke magana kan kafa kungiyar, Shugabanta Farfesa Umar Labdo, ya ce kungiyar ba ta Fulani ne kadai ba ce, amma dukkan makiyaya, daga kowanne kabila, yanki da addini.

Ya ce kungiyar za ta zama murya ga makiyaya da ba su da karfin fada a ji inda za su iya yi wa kasa bayanin matsalolinsu da bukatunsu da abin da suka fatan cimmawa.

Exit mobile version