Site icon Muryar 'Yanci

Ta Faru Ta ?are: Wanda Ya Shigar Da ?arar Rahama Sadau Ya Janye

Shahararren mai rajin kare hakkin dan Adam Muhammad Lawal Gusa, ya janye karar da ya shigar a kan fitacciyar jaruma Rahama Sadau, bayan ta fitar da wani hoto da ya janyo batanci ga Annabi (S.A.W) a shafin ta na yanar gizo.

Muhammad Lawal Gusau, ya bayyana janye karar ne a cikin wata takarda da aike wa shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna, inda ya ce hakan ya biyo bayan matsayar da manyan malamai su ka dauka ne dangane da lamarin.
Haka kuma, Lawal Gusau ya aika takardar zuwa ga wasu manyan malamai, wadanda su ka hada da limamin masallacin Sultan Bello Shiekha Khalid Sulaiman, da na masallacin Al-Mannar Shiekh Muhammad Tukur Adam Abdullahi, da na masallacin Dahiru Bauchi Shiekh Abdulkadir Hashim Bindawa da kuma Shiekh Halliru Maraya.

Muhammad Lawal Gusau, ya ce ya janye karar ne, sakamom fahimtar da aka samu, da kuma nadamar da jarumar ta yi, inda ta sha alwashin cewa haka ba za ta kara faruwa ba da izinin Allah.

Malaman addini dai sun bayyana mahimmancin ba Rahama Sadau uziri, musamman ganin yadda ta nuna damuwa da kuma nadamar abin da ta aikata.

Exit mobile version