An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966.
Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990.
Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka:
Laftana – ranar 27 ga Satumba 1990
Kyaftin – ranar 27 ga watan Satumba 1994
Manjo – ranar 27 ga watan Satumba 1998.
Laftanar Kanar – ranar 27 ga watan Satumba 2003.
Kanar – ranar 27 ga watan Satumba 2008
Birgediya Janar – ranar 27 ga watan Satumba 2013
Manjo Janar – ranar 27 ga watan Satumba 2017.
Sabon babban hafsan sojin kasan na Najeriya ya yi karatun digirinsa na farko a fannin Tarihi sannan ya yi digiri na biyu wato Masters a kan harkokin siyasar kasashen duniya da difilomasiyya.
Ya rike mukamai daban-daban ciki har da mataimakin sakataren rundunar soji da kuma sakataren na rundunar soji a hedikwatar sojin kasa.
Mukamin da ya rike na karshe kafin na?in nasa shi na jagorantar ya?i da Boko Haram karkashin rundunar Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya ta?a ri?e mu?amin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko wato General Officer Commanding (GOC) 1 Division.
Kafin nadinsa a mukamin General Officer Commanding 1 Division, Manjo Janar Yahaya ya jagoranci runduna ta 4 da ke hedikwatar rundunar sojin Najeriya.
Kazalika ya rike mukamin Kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, a jihar Borno.
A shekarar 2019, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jagoranci rundunar Operation CLEAN SWEEP wadda ta fatattaki ‘yan bindigar da ke dajin Kuduru a Birnin Gwari na jihar Kaduna.

