Mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya yi tir gami da Allah wadai da sace ?aruruwan ?aliban makarantar Sakandaren Kimiyya ta kwana dake ?aramar Hukumar ?an?ara da wasu ‘yan Bindiga suka yi a jihar Katsina a ?arshen Mako.
An ruwaito cewa Sarkin Musulmin ya yi wannan furuci ne a cikin wani jawabi da aka fitar a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, ta hannun babban sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam Dr Khalid Aliyu.
Sarkin Musulmin yace lamarin ya nuna matsaloli a tsarin tsaron Najeriya wanda akwai bukatar magance su cikin gaggawa.
Ya ce satar daliban ya kasance abun bakin ciki, musamman da yake zuwa a daidai lokacin da ake juyayin kisan da aka yi wa alumma a Zabarmari.
Ya yi korafin cewa karfin gwiwar da ‘yan bindigar suka samu na aiwatar da satar daliban a ranar da Shugaban kasar ya isa jihar Katsina ya kara nuna halin da gwamnatinsa ke ciki.
Don haka kungiyar, ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya amsa koken yan Najeriya na sauya fasalin tsaro da yin jawabi ga kasar.
Akwai rade radin cewa saboda wasu dalilai na son zuciya, wasu manya a hukumomin tsaro basa so a kawo karshen rashin tsaro. Idan ba haka ba, ta yaya mutum zai yi bayani game da zirga zirgan daruruwan yan bindiga a kan Babura ba tare da an gane su ba.
Ya bayyana cewa abunda yafi ba kungiyar JNI mamaki shine gazawar gwamnati wajen gano ainahin mafakar makiyan, gano inda karfinsu yake da kuma amfani da duk wani dama wajen kakkabe su ko durkusar da su.

