Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci kungiyar malaman jamioi da sauran kungiyoyin maaikata da su rungumi sulhu da gwamnati tare da gudun yajin aiki a matsayin hanyar neman a biya musu bukatu.
Buhari ya bayyana hakan ne a taro na 74 na yaye dalibai a jamiar Ibadan a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba shekarar da muke ciki ta 2022.
Shugaba Buhari ya samu wakilcin farfesa Abubakar Rasheed ne a taron, wanda shine babban sakataren hukumar jamioi ta kasa (NUC).
Buhari ya kuma yaba da kokarin gudunarwar jamiar Ibadan bisa kare martabar jamiar a idon duniya.
Ya kuma yaba da kokarin jamiar wajen yaye ?alibai masu digiri na farko masu nagarta da ke sanya kasa alfahari a ciki da wajen kasar nan.
Yajin aiki na taba tattalin arziki da nagartar karatu, ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar ladabtarwa da tabbatar da halaye na gari a dukkan jamioin kasar nan domin ciyar da kasar nan gaba. Ya shaida cewa, ya kadu da yadda kungiyoyin jamioi a kasar nan suka daura damarar fada da gwamnati a wannan shekara ta 2022.
Shugaban ya ce sabanin da ke tsakanin gwamnati da malaman na da matukar tasiri mai muni ga tattalin arzikin kasar nan, musamman duba da yadda hakan ke shafar zangon karatun dalibai.

