Site icon Muryar 'Yanci

Sokoto: Jama’ar Gari Sun Babbake ‘Yan Bindiga ?urmus

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu fusatattun matasa sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ta hanya banka musu wuta a yayin da suka yi yunkurin kai hari a yankin Goronyo a ranar Laraba.

Matasan sun kuma ?ona ofishin ?an banga da aka fara ajiye wadanda ake zargin. Yan bindigan sun zo wata Rugar Fulani da ke wajen Goronyo cikin dare domin su sace shanu amma mutanen suka yi fito-na-fito da su suka kama uku cikinsu.

“Mutanen a shirye suke. Harsashi baya ratsa su. Sun dakile harin kuma suka kama uku cikin yan bindigan suka mika su hannun ?an banga da safe, in ji wani mazaunin garin.

“Da labarin ya isa wurin matasan mu, sun taru sun tafi ofishin ?an banga da aka ajiye su a Goronyo. “Kalaman da ke fitowa bakin ?ar bindigan ya fusata su inda ta ke cewa ba yau aka fara kamata ba kuma ta san za a sake ta.

“Wannan ne ya ?ata musu rai, suka fi karfin ?an bangan suka cinnawa ofishin wuta. “Daya daga cikin wanda ake zargin ya mutu a ofishin yan bangan, macen da ?ayan na mijin sunyi yunkurin tserewa amma aka kama su aka kashe su aka ?ona gawarsu,” a cewar wani ganau.

Shugaban ?aramar hukumar, Abdulwahab Yahya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce jami’an tsaro suna sintiri domin tabbatar da doka da oda. A cewarsa, ?an bindiga sun dade suna sace shanu a yankin duk da jami’an ?an sanda 60 da ke garin.

Kakakin ?an sandan Sokoto, ASP Sanusi Abubakar shima ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ce ba shi da cikakken bayani a lokacin ha?a wannan rahoton.

Exit mobile version