Hukumar NDLEA mai ya?i da miyagun ?wayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani tsohon soja mai shekara 90 da zargin yi wa ‘yan fashin daji safarar ?wayoyi a Jihar Sokoto.
Wata sanarwa ta ce an kama Usman Adamu ne ranar Laraba, 3 ga watan Agusta a garin Mailalle na ?aramar Hukumar Sabon Birni.
“An kama shi da tabar wiwi mai nauyin 5.1kg,” a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.
Kazalika a ranar Alhamis, hukumar ta kama wata mota a JIhar Zamfara ma?are da ?wayar Diazepam 50,000 a kan hanyarta ta zuwa Sokoto daga birnin Benin na Jihar Edo, wanda ta ce mallakar wani ne mai suna Umaru Attahiru.
A wani binciken na daban, NDLEA ta dam?e wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong da duro uku na ?wayar crystal methampetamine – wadda ake kira Mkpuru Mmiri a Najeriya.
Kayan da NDLEA ke zargin an shiga da su ne daga Indiya, an kama su yayin da ake shirin kai su wani wuri a birnin Legas lokacin da aka tare motar da ke ?auke da su.

