Site icon Muryar 'Yanci

Sojojin Ha?in Gwiwa Sun Hallaka Masu Ikirarin Jahadi Ba Adadi A Nijar

Jami’an soji a Burkina Faso da Nijar sun ce an kashe ?an bindiga da dama masu da’awar jihadi a wani samamen ha?in gwiwa da aka ?addamar a iyakokin ?asashen biyu.

Kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito wata sanarwa da ta ce an kashe maya?a kusan 100 a farmakin na mako biyu da ya ?unshi ?aruruwan sojoji.

Rahotannin sun ce an kwace makamai, da bama-bamai da aka kera a gida da kuma babura sama da 100.

Mayakan masu da’awar jihadi da ke addabar ?auyukan ?asashen biyu da na Mali – galibi suna amfani da babura ne yayin kai hare-hare.

A farkon watan Yuni sama da mutane 170 aka kashe a wasu kauyuka biyu da ke arewa maso gabashin Burkina Faso – hari mafi muni a cikin shekaru.

Gwamnati ta zargi masu da’awar jihadi – wasu daga cikinsu ta ce yara ne ?an shekara 12.

Exit mobile version