Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Dakarun rundunar soji sun kashe ‘yan fashi “masu yawa” a ?aramar Hukumar Talata Marafa ta Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Onyema Nwachuku, ta ce dakarun sun yi arangama ne da ‘yan bindigar a yankunan Mayanchi da Dogo Karfe da Fagantama, inda suka yi nasarar kashe da yawa daga cikinsu sannan suka ?wace bindiga ?aya da harsasai masu yawa.
A wata fafatawar daban, sojojin sun kashe ‘yan fashi biyar a ?auyen Bingi na ?aramar Hukumar Bungudu ta Zamfarar tare da jikkata wasu da dama.
Kazalika, sojojin sun ?wace bindigar AK-47 ?aya da babur ?aya da wayoyin salula uku.
Da safiyar Juma’a ne mazauna Bingi da kewaye suka toshe hanyar shiga garin Gusau daga Sokoto don nuna fushinsu game da hare-haren ‘yan bindigar, suna masu cewa sojojin da ke gadin ?auyukan nasu sun fice daga garin.
Sai dai wani mazaunin yankin ya fa?a wa BBC a safiyar Asabar cewa mutanen, wa?anda akasarinsu mata ne da yara, sun koma garuruwansu bayan jami’an tsaron sun koma.
