Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a yau Talata ne ake sa ran Kotun ?aukaka ?ara za ta yi zaman sauraron ?arar rikicin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da ?angaren Sanata Ibrahim Shekarau.
?angaren Gwamna Ganduje ne ya ?aukaka ?arar bayan ya sha kaye a shari’o’i biyu da suka gabata, inda yake neman a soke shugabancin Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Shekaru, sannan a bayyana Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaba.
A wata shari’ar ta kotun tarayya na baya, kotun ta bayyana cewa ?angaren Ganduje ba shi da hurumin neman a kori ?arar saboda ya riga ya ?aukaka ?ara a Kotun ?aukaka ?ara, saboda haka ne kuma ta yi watsi da bu?atarsu.
Rikicin APC a Kano ya samo asali ne tun bayan gudanar da tarukan jam’iyyar a matakin maza?u da jiha, abin da ya haddasa aiwatar da taruka biyu ?ar?ashin Sanata Ibrahim Shekarau da kuma ?angaren gwamnatin Kano.

