Site icon Muryar 'Yanci

Siyasa: Wike Ne Matsalar Jam’iyyar PDP – Mustapha Inuwa

IMG 20240710 WA0038

?aya daga cikin jagororin jam’iyyar PDP a jihar Katsina kuma tsohan sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya bayyana cewa duk matsalolin da jam’iyyar PDP ke ciki a kowacce jiha har ma da kasar baki daya, Ministan Abuja kuma tsohan gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya jefata, saboda shi ke juya ragamar jam’iyyar PDP daga waje kuma jam’iyyar APC ya ke yi wa aiki.

Malam Mustapha Inuwa ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa ta musamman da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP kan zaben shugabannin jam’iyyar a kowane mataki da ke tafe, wanda ya gudana a ofisoshinsa dake hanyar Mani a cikin garin Katsina, yau Lahadi.

Tsohan Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya kara da cewa mu gayawa kanmu gaskiya, hatta PDPn ta kasa daga waje jam’iyyar APC ke juyata, saboda tsohan gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike shi ke juyata a halin yanzu, sai abinda ya ce shi ake yi kuma minista ne a karkashin shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar PDP.

Exit mobile version