?an takarar shugaban ?asa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya za?i Doyin Okupe a matsayin mataimakinsa na ri?o kafin ya yanke shawarar wanda zai za?a.
LP ta mi?a sunan Mista Okupe ga hukumar za?e INEC yayin da wa’adin da hukumar ta bai wa jam’iyyu ke ?arewa a daren yau Juma’a.
Hakan na nuna ?an takarar ya yi kamanceceniya da takwaransa na jam’iyyar APC mai mulki Tinubu wanda ya ?auki Musulmi mataimaki, inda shi kuma ya ?auki Kirista mataimaki.
Doyin Okupe, shi ne tsohon mai tamaka wa tsohon Shugaban ?asa Goodluck Jonathan kan kafofin ya?a labarai.
“Yanzu haka da nake magana da ku, ni nake ri?e da mataimakin ?an takarar shugaban ?asa na jam’iyyar Labour Party,” a cewar Okupe yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yau Juma’a.
Okupe ya tabbatar da cewa Mista Obi na ci gaba da shawarwari game da wanda zai za?a a matsayin abokin takarar tasa.
Hukumar ta saka Juma’a 17 a matsayin rana ta ?arshe da jam’iyyu za su mi?a mata sunayen ‘yan takarar da suka za?a da za su wakilce su a za?en 2023, amma suna iya sauya sunayen mataimakan ‘yan takarar.

