A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jamiyyar Labour, Peter Obi, ya umarci jamian tsaro na SSS, da su kulle shi a otel na tsawon awanni 48 a jihar.
Mista El-Rufai ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2013 lokacin da ya je jihar a matsayin jamiin sanya ido na jamiyyar APC, domin shaida zaben maimai na gwamnan jihar Anambra.
El Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin hadin gwiwa na yankin Kaduna ranar Litinin tare da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC, Bola Tinubu.
Ko da ya ke El-Rufai ya ce yana da dukkanin jamian tsaro a hannunsa a matsayinsa na gwamnan jihar Kaduna a yanzu domin ya rama zaluncin da aka yi masa, amma ba zai rama mugunta da mugunta ba.
A shekarar 2013 na je jihar Anambra a matsayin jamiin jamiyyar APC domin shaida zaben fidda gwani na gwamna. Bakonku, Peter Obi, shine gwamna a Lokacin. Ya sa a ka tsare ni na tsawon awanni 48 a dakin otal di na.
Yanzu ni ne gwamnan jihar Kaduna. Kuma yana zuwa Kaduna, ban da yan sanda da SSS, ina da shiyya-shiyya guda daya na rundunar sojojin Nijeriya a nan idan ina bukatar kamawa da tsare kowa. Amma mu yan Arewa ne, muna da wayewa, ba ma yin haka.

