Site icon Muryar 'Yanci

Shugabancin Kasa: Gwamnoni Sun Nuna Goyon Baya Ga Osinbajo

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam’iyyar APC da dama ne aka hango a fadar shugaban kasa inda suka gana da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Gambari, lamarin da ake ganin cewa ka iya zama wani yunkuri na samun amincewar dan takarar shugaban kasa na sulhu.

Rahotannin sun ce da alama akasarin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo, gabanin zaben-fidda gwani.

Gwamnonin sun gudanar da tarurruka da dama a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke Asokoro, Abuja, a ranar Talata, bayan sun gana da Buhari.

Exit mobile version