Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Bangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta na jam’iyyar APC a Jihar ya ce za su tafi Kotun Koli don ci gaba da kalubalantar bangaren su Gwamna Ganduje a rikicin APC na Kano.
Tsohon gwamnan Kanon ya kuma nuna rashin jin dadinsa da wasu kalmomin batanci da ya ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da su jim kadan bayan hukuncin kotu da ke cewa bangaren gwamnan ke da halastaccen shugaba.
A ranar Alhamis ne dai kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ga Abdullahi Abbas, kuma sa’o’i da yanke wannan hukuncin uwar jam’iyya ta kasa ta mika masa takardar shaidar shugabanci, matakin da bai yi wa ?angaren Shekarau dadi ba.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce uwar jam’iyya ta nuna rashin adalci kuma sun yi mamakin irin kalaman da suka fito daga bakin Gwamna Abdullahi Ganduje.

